Isa ga babban shafi
China

Girgizan kasa ta kashe mutane 150 a China

Rahotanni daga kasar China sun ce akalla mutane 150 suka mutu, wasu da dama suka samu rauni sakamakon girgizan kasa da ta shafi yankin Yunnan mai tsaunuka a kudu maso yammacin kasar. Kamfanin dillacin labaran China ya ruwaito cewa gidaje da dama ne suka rushe tare da danganta girgizan kasar a matsayin mafi muni da aka taba gani a tsawon shekaru 14 a kasar China.

Yankin Yunnan mai tsaunika da Girgizan kasa ta shafa a kasar China
Yankin Yunnan mai tsaunika da Girgizan kasa ta shafa a kasar China REUTERS
Talla

An kwashe daruruwan mutane daga gidajensu a yankin saboda girgizan kasa da ta haifar da katsewar wutar lantarki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.