China
‘Yan sanda sun kama masu zanga zanga 500 a Hong Kong
‘Yan sanda a Hong Kong, sun cafke masu zanga zanga 500 da suka yi bore domin neman ganin an kawo sauyi a na tsarin dimokradiya.
Wallafawa ranar:
Talla
Kama mutanen ya biyo bayan wani babban gangmi lumana da aka yi a ranar talatar da ta gabata.
Rahotanni sun nuna cewagangamin ya sa an samu turuwar mutanen da ba a taba ganin irinsa ba tun bayan da Birtaniya ta mika yanking a China a shekarar 1997.
‘Yan sanda sun ce an kama mutane ne bisa laifin yin gangami ba bisa ka’ida ba, lamarin day a rutsa da masu fafutukar ganin an kafa tsarin dimokradiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu