Isa ga babban shafi
Hong kong

Mutane 11 sun jikkata a harin da aka kaiwa Fasinjojin Mota a Hong Kong na kasar China.

Wani mutum mai shekaru 57 ya kai hari wa Pasinjojin wata Motar Bus da Adda a yankin Hong kong. Maharin dai ya jikkata mutane 11 kamin daga bisani Pasinjojin suka kama shi suka kuma yi mashi duka.

Hanyar Danube
Hanyar Danube REUTERS/Szabo H. Sandor/ORFK/Handout
Talla

Wannan al’amarin da ya auku a birnin da ake ganin yafi ko wane tsaro a Duniya, ya kai ga kwantar da mutane 11 a Assibiti, kuma dai daga cikin su ta rasa dayan Yatsanta.

Harin dai ya faru ne da misalin karfe 7;30 na Safiya, akan babban Titi dake a Kauyen Tuen Munn a birnin Hong Kong, kuma daukacin mutanen dake cikin Motar Ma’aikatan wani Kamfani ne mai sarrafa ‘ya’yan Itatuwa.

‘Yan sanda sun bayyana cewar harin mutumin ya kuma shafi wasu ‘yan uwansa biyu dake zaune a cikin dan lungu lokacin da ya tare Motar.

Kuma sun bayyana samun wata Adda da suke kyautata zaton cewar da ita mutumin ya dinga sarar Pasinjojin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.