Isa ga babban shafi
Malaysia-China

Malaysia na zargin wasu ne suka sace jirgin sama dauke da mutane 239

Yayin da kasshen duniya ke ci gaba da binceken inda jirgin saman kasar Malaysia daya bace da fasinjoji 239 ya shiga, hukumomin kasar sun ce suna da yakinin cewa da gangana aka juya akalar jirgin zuwa wani wajen na daban. Bayanai sun nuna cewa wani ko wasu ne suka kashe na’urorin sadarwan jirgin, aka kuma juya akalar shi zuwa yamma, inda ya yayi tafiyar sa’oi da dama, kafin a daina jin duriyar shi.Wannan ya sa ake ci gaba da nuna damuwa kan makomar jirgin da ma fasinjojin da ke ciki.Lokacin da yake hira da manema labaru Priministan Malaysia Najib Razak ya ki yin amfani da kalmar fashin jirgi, sai dai yace yanzu masu bincike na nazarin kam matuka da fasinjojin da ke cakin jirgin. 

wani jirgin kamafnin jiragen kasar Malaysia
wani jirgin kamafnin jiragen kasar Malaysia
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.