Isa ga babban shafi
Malaysia-Vietnam-Indiya

Indiya ta shiga aikin binciken jirgin saman kasar Malaysia

Yau Laraba sojan ruwan kasar india sun shiga aikin cikiyar jirgin saman kasar Malaysia, daya bace da fasinjoji 239 tun ranar Asabar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin kasar Vietnam suka bayar da sanarwar dakatar da aiki neman jirgin ta sama.Sufeto janar na rundunar sojan ruwan kasar India ya shaidawa kanfanin dillacin labarum Faransa na AFP cewa an umarce su, su shiga aikin neman jirgin da ya bace, a tsakanin tsibiran Andaman da Nicobar.Tsibiran 2, mallakin Indiya ne, sai dai suna da nisan daya kai kilimita 1,000 daga doron kasa, a cikin kasar ta Indiya, kuma sun fi kusa da gabar tekun kasar Myanmar.Mai magana dayawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Indiya Syed Akbaruddin yace hukumomin kasar ta Malaysia sun amince da tayin kasar, na bayar da tallafi a aikin binciken jirgin.A halin da ake ciki kuma, Vietnam, da aka mayar da hankali wajen binciken jirgin a kudancinta ta, ta bayar da sanarwar dakatar da aikin binciken ta sama. kasar tace zata ci gaba da aikin binciken a ruwa, har zuwa lokacin da hukumomin kasar Malaysia su bayyana sabuwar alkiblar da za a dauka a aikin binciken da kasashe da dama ke bada tallafi.Zuwa yanzu bayanai sun fara fitowan kan kalaman karshe da aka ji matun jirgin ya yi da masu kula da zirga zirgar jirage, inda ya yi sallam da su masu kula da jami’an kasar Malaysia, a daida lokacin daya shiga kasar Vietnam. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.