Isa ga babban shafi
Habasha-Switzerland

Mataimakin matuki ya sace jirgin saman kasar Habasha

Jami’an tsaron kasar Switzerland sun samu nasarar murkushe wani mutum da ya yi yunkurin fashin jirgin saman daukar fasinja mallakin kamfanin jiragen saman kasar Habasha, bayan da jirgin ya sauka a birnin Geneva. Hukumoni sun bayyana mamakin kan yaddda lamari ya faru.A nasu bangaren, hukumomin kasar Habasha sun bayyana Hailemedehin Abera Tagegn, mai shekaru 31, da ke aiki a matsayim mataimakinm matukin jirgin, da kuma ya shafe shekaru 5 yana aiki da kamfanin a matsayin wanda ya yi awon gaba da jirgin.Jirgin kirar Boeing 767, mallakin kamfanin Ethiopian Airlines, ya baro birnin Adis Ababa kasar Habasha ne, ya nufi Roman kasar Italiya da misalin karfe 4 na safe kafin Abera Tagegn ya yi fashin sa.Ministan yada labarum kasar, Redwan Hussein yace jirgin na dauke da ‘yan kasar italiya 139, Amurkawa 11, Habashawa 10 gami da ‘yan kasashen Nigeria, Romania, Faransa, Ireland, Jamus da ma sauran kasashe.Hukumomin sun kara da cewa ba a taba samun mutumin da aikata wani mugun laifi ba, kuma bashi da tarihin matsalar tabin hankali, sai dai a cewar su ana ci gaba da bincike don gano ko akwai wata matsalar. 

Jirgin kamfanin Ethiopian Airlines da aka sace
Jirgin kamfanin Ethiopian Airlines da aka sace
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.