Yemen
An kashe wani babban jami'in sojan Rasha a kasar Yemen
Wasu ‘yan bindiga akan babur sun buda wuta inda suka kashe wani babban jami’In sojan kasar Rasha da ke aiki a birnin Sana’a na kasar Yemen a sanyin safiyar yau.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Talla
Rahotanni daga birnin na cewa, lamarin ya faru ne a wajen wani Hotel a daiai lokacin da jami’in soja da ke bai wa rundunar sojan kasar ta Yemen Shawara ke shirin barin Hotel din zuwa wani wuri.
To sai dai duk da cewa kawo yanzu ba wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai wannan hari, tuni aka danganta haka da kungiyar Alka’ida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu