An kaiwa Firaministan Yemen Basindawa harin kisa
Firaministan kasar Yemen, Mohammed Basindawa, ya tasallake rijiya da baya lokacin da wasu ‘Yan bindiga suka bude wa tawagar motarshi wuta a cikin Sanaa a dai dai lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa gida.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran Faransa, ya ruwaito cewar, ‘yan bindigan guda hudu sun bude wuta ne akan tawagar dake wucewa a tsakiyar birnin, sai dai babu wanda yaji rauni a ciki.
Wannan shine karo na farko da aka kaiwa shugaban hari, wanda ke jagorantar ‘yan adawa a karkashin gwamnatin Shugaba Ali Abdullah Saleh.
Kuma tarihi ya nuna cewa an jima ana kaiwa mambobin gwamnatinshi harin kisa a baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu