Isa ga babban shafi
India

Ma’aikata sun kaddamar da Zanga-zanga a India

Dubban ma’aikata ne suka fito domin gudanar da zanga zanga a kasar India, don nuna adawarsu da wasu sauye sauyen Gwamnati da suka ce sun yi karo da manufofin ma’aikatun kasar.

Matafiya rike da kayansu bayan kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki a kasar India
Matafiya rike da kayansu bayan kungiyoyin kwadago sun shiga yajin aiki a kasar India REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Ayyukan yau da kullum da suka hada da sufuri, sun tsaya cak, sakamakon yajin aikin da kungiyoyi kwadago 11 suka fara, don adawa da sauye sauyen Gwamnati da suka hada da yadda ake gudanar da kasuwanci, al’amarin da ya haifar da hauhawan farashin kayan masarufi da man fetur.

Sakatare Janar na kungiyoyin ma’aikatan, Tapan sen, yace sun shiga yajin aikin ne saboda kunnen uwar shegun da gwamnatin kasar ta yi game da bukatunsu, wadanda suka hada da kara kudin Mai da gas na girki.

Sakataren ya ce matakin wata dama ce ta bai wa masu karfi da attajirai damar jefa talakawan kasar cikin halin kunci.

Sai da ya sanar da cewa, akalla ma’aikata sama da miliyan 100 za su shiga yajin aikin na kwanaki biyu, wanda zai hana zirga zirgar jiragen kasa da motoci, tare da rufe Bankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.