Isa ga babban shafi
Falestine-Isra'ila

Falesdinawa sun nemi sabuwar Gwamnatin Isra’ila ta amince da ‘Yancinsu

Falesdinawa sun ce za su yi aiki tare da sabuwar Gwamnatin Isra’ila wajen samar da zaman lafiya a tsakaninsu idan sabuwar Gwamnatin za ta amince da ‘Yancinsu.

Tutar Isra'ila a kan iyakarsu da Isra'ila
Tutar Isra'ila a kan iyakarsu da Isra'ila REUTERS/Ammar Awad
Talla

Minsitan Harkokin Wajen Falasdinu, Riyad al – Malki ne ya bayyana hakan a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, inda ya ce, hanyar cim ma zaman lafiya ita ce amincewa da yarjejeniyar shata kan iyakokin da bangarorin biyu suka amince a 1967.

Kazalika, Mista al Maliki yace Falasdinawa za su shigar da kara a kotun ICC idan Isra’ila ta ci gaba da gina sabbin gidaje a yankunansu.

A ranar Talata ne Firaministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya sake lashe zabe na wani sabon wa’adi, a wani zabe da ya kasance zazzafa.

Sai dai Ministan harkokin wajen Fasadinu, ya ce irin halayyar da Netanyahu ya nuna bayan da mambobin Majalisar Dinkin Duniya suka amince da Palasdinu a matsayin mamba ‘yar kallo, ya sabawa irin yunkurin da a ke yi na shawo kan rikicin bangarorin biyu, inda ya yi nuni da kashe kashen da kasar ta aikata a yankin Gaza da kuma gina sabbin matsugunai.

Sai dai wakilin kasar Isra’ila a zauren Majalisar Dinkin Duniyan, Ron Prosor, ya soki wannan kalamai na Malki, inda ya zargi shugabannin Falasdinawan da rashin gayawa jama’arsu gaskiya akan yadda za a shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.