Isa ga babban shafi
Syria

Shugaba Assad ya gabatar da matakan kawo zaman lafiya a Syria

Shugaban kasar Syria Bashar Assad ya gabatar da matakai uku da yake ganin sune kadai za a bi domin kawo karshen rikicin kasar da ya zuwa wannan lokaci akayi hasarar rayukan mutane sama da dubu 60. Da farko Shugaba Bashar Assad yace akwai bukatar tuntuban jamaan kasar baki daya, da suka hada da kungiyoyi da jamiyyun siyasa dake ciki da wajen kasar.  

Shugaban kasar Syria, Bashar al - Assad
Shugaban kasar Syria, Bashar al - Assad
Talla

Na biyu injishi, masu kaunar kasar su zauna a tattauna tsarin yadda ake son kasar ta kasance, inda daga bisani za a gabatar da matsayin taron domin zaben raba gardama.

Sannan kuma inji Shugaba Bashar Assad mataki na uku, shine a kaddamar da sabuwar Gwamnati karkashin kundin tsarin mulkin kasar, sannan a yi taro na kasa domin yafewa juna, da sake gina kasar da akayi raga-raga da ita a tsawon watanni 21 da akayi ana bata-kashi.

Sai dai kuma tun ba a kai ko'ina ba bangaren ‘Yan adawan kasar, ta bakin Kakakinsu Walid Al-Bunmi, sun fito fili sunce sam zance kawai ne, domin jawabin Shugaban kame-kame ne kawai yakeyi.
 

Kasashen duniya dai nata maida martani gameda bayanan Shugaban, ciki har da kasar Amurka wacce daga baya-bayan nan ta yi watsi da jawabin inda ta ce wata dabara ce da shugaba Assad ya ke so yabi domin zama a karagar mulki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.