Mutane 60,000 suka mutu a Syria, inji MDD
Kwamishinan hukumar kare Hakkin Bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay yace Akalla mutane 60,000 suka mutu a rikicin Syria da aka shafe shekaru Biyu ana yi tsakanin Gwamnati da masu adawa da Shugaba Bashar al Assad.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar da wadannan alkalumman ne a dai dai lokacin da aka samu karin wasu mutum 12 da suka mutu sakamakon wani kazamin harin da aka kai a wani kauye kusa da birnin Damascus.
Navi Pillay ya bayyana wa babban taron Geneva cewar kamin watan Nuwamban bara, akalla mutune dubu Hamsin da Tara ne aka kashe a yakin da aka kwashe watanni 21 ana gwabzawa.
Rikicin Syria dai ya ya faro ne daga zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Bashar Assad a watan Maris na shekarar 2011.
Sai dai majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar yawan wadanda suka mutu a rikicin na Syria ya fi karfin hasashen su amma kuma abin ban tsoro ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu