Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Mutanen Korea ta Kudu suna jefa kuri’ar zaben shugaban kasa

Al’ummar kasar korea ta Kudu sun fito kwansu da kwarkwata domin zaben shugaban kasa inda ake sa ran za su ba Mace damar shugabantarsu. Park Geun-Hye, ‘Yar tsohon shugaban kasar ce Park Chung-Hee, kuma tana takara ne da Moon Jae-In wanda mahaifinsa dan gudun hijira ne daga Korea ta Arewa.

Dubban mutanen Korea ta Kudu da suka fito domin kada kuri'ar zaben shugaban kasa
Dubban mutanen Korea ta Kudu da suka fito domin kada kuri'ar zaben shugaban kasa RFI / Stéphane Lagarde
Talla

Duk shugaban da aka zaba a fadar Blue House sai ya yi kokarin magance matsalar tattalin arzikin kasar da ke tafiyar hawainiya da kuma rikicin kasar da Korea ta Arewa.

Park mai shekaru 60 idan an zabe ta za ta kasance shugaba mace ta farko a fadar Blue House.

A shekarar 1979 ne wani jami’in leken asirin Korea ta Arewa ya kashe Mahaifin Park bayan wasu magoya bayan Korea ta Arewa sun kashe mahaifiyarta.

Mista Moon mai adawa da Park Lauya ne kuma dan rajin kare hakkin Bil’adama wanda aka daure a zamanin mulkin Park Chung-Hee.

Hukumar Zabe tace kashi 65.2 suka fito kada kuri’ar zaben fiye da wadanda suka fito kada kuri’a a zaben shugaban kasa da aka gudanar a shekarar 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.