Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Moon ya rasu yana mai shekaru 92

Shugaban Majami’ar da aka wa lakabi da Unification Church wacce aka fi saninta da auren gama gari da kuma gudanar da harkokin kasuwanci, kasar Korea ta Kudu, Sun Myun Moon, ya rasu yana mai shekaru 92. 

Marigayi Sun Myung Moon da matarsa
Marigayi Sun Myung Moon da matarsa Wikipedia
Talla

Ya rasu ne dalilin ciwon Pneumonia da ya yi ta fama da shi a cikin makwani biyu da su ka wuce a asibitin da ke hedkwatan majami’ar Gapyeong a gabashin birnin Seoul.

Wasu da dama dai a cikin mabiya addinin Kirista na ma Moon kallon wani Malami mai ci addini da kuma gudanar da kungiyoyin sirri da kuma gudanar da wasu harkokin kasuwanci da hukuma bata amince da su ba, wanda hakan ya taba sa aka kulle shi a kasar Amurka.

Majami’ar Moon kan hada aure tsakanin mutane da ba yarensu ko jinsi daya ba, hasali ma ma’auratan kan hadu ne ranar daurin aurensu bayan Moon ya hadasu tun farko.

Akan kuma taru ne a wani babban filin wasa don gudanar da auren.

A lokacin mutuwarsa, an yi kiyasin ya na da mabiya sama da miliyan uku, koda ya ke ana ikrarin cewa yawan nasu ya ragu tun cikin karnin shekarun 1980.

A lokacin da ya rasu, Moon, ya kasance yana kwance ne a dakin gobe da nisa, inda aka saka masa na’urori da ke taimaka mai.

Izuwa lokacin hada wannan rahoto babu wata sanarwa da ta fito daga gwamnatin kasashen Korea ta Kudu da kuma ta Arewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.