Isa ga babban shafi
MDD-Syria-China-Rasha

China ta Mayar da Martani kan dakile Kudirin MDD game da Syria

Kasar China ta yi watsi da zargin da Amurka ke mata na kare Gwamnatin Syria, wajen hawa kujerar naki a Majalisar Dinkin Duniya.Yayin da take kare kanta daga zargin da Amurka da kasashen Yammacin duniya ke mata, China ta ce bata gamsu da shirin kasashen Yammacin duniya ba, kan Syria, saboda haka ta dauki matakin hawa kujerar naki. 

REUTERS
Talla

China ta ce 'yan kasar Syria ne kawai zasu iya magance rikicin dake addabar su, wajen tattana a tsakaninsu, amma ba anfani da karfin soji ba, kamar yadda akayi a Libya.

Ta kara da cewa, goyawa bangare daya baya, akan daya bangaren ba manufa ce mai kyau ba, domin hakan zai haifar da babbar matsala.

Kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa da Jamus, sun jagoranci kasahsen duniya wajen sukar matsayin China da Russia, na kin basu goyan bayan daukar mataki kan Syria a Kwamitin Sulhun MDD, matakin da China da Russia suka yi watsi da shi.

Kasashen Yammacin duniya dana Larabawa na ci gaba da nuna bakin cikin halin da ake ciki a kasar ta Syria, yayin da Rasha da China suka toshe kudirin Kwamitin Sulhun MDD dake neman Shugaba Bashar al-Assad ya ajiye madafun ikon kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.