Isa ga babban shafi
Syria

Ana Mayar da Martani kan dakile Kudirin MDD kan Syria

Kasashen Yammacin Duniya sun nuna fusata kan yadda kasashen Rasha da China suka hau kejerar naki a Kwamitin Sulhun MDD, kana kudirin da yayi tir da matakan da gwamnatin Siriya ke dauka, domin dakile masu zanga zanga.Amurka tace haka abun kunya ne, yayin da Birtaniya ke cewa haka ya nuna dakile fafatukar Siriyawa, itama kasar Faransa ta yi tir da matakin toshe kudirin Kwamitin Sulhun na MDD.

AFP / UN PHOTO / Eskinder Debebe
Talla

Kasashen China da Rasha sun ce kudirin bai yi la’akari da dukkanin sassan ba.

Watsi da Kudirin yazo sa’oi bayan masu fafatuka na kasar ta Siriya sun bayyana mutuwar mutane 55 a garin Homs.

Yayin da kasashen Yammaci dana Larabwa ke nuna rashin jin dadi da toshe kudirin MDD kan kasar Siriya, gwamnatin kasar Tunisiya ta daukan matakin janye amincewa da gwamnatinta Siriya karkashin Shugaba Bashar Al-Assad.

Jim kadan da aiyana matakin, ofishin jakadanci Siriya dake birnin Tunis, yayi kasa kasa da tuta, abunda ya janyo shewa da jin dadi daga masu zanga zanga.

Juyin juya halin da kasashen Larabawa ke fuskanta, ya faro daga kasar ta Tunisia dake yankin Arewacin Afrika.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.