Isa ga babban shafi
MDD-Syria-China-Rasha

China da Rasha sun hau kujerar na-ki game da Syria

Kasar China ta kare matakinta na hawa kujerar na-ki game da daftarin Majalisar Dinkin Duniya da ke bukatar shugaban kasar Syria Bashar al-Assad bankwana da madafan ikon kasar, kamar yadda hukuncin Majalisar akan Libya ya sabawa kasar China.

Jekadan kasar Syria Bashar Ja'afari yana ganawa da Jekadan kasar China a Zauren Majalisar Dinkin Duniya.
Jekadan kasar Syria Bashar Ja'afari yana ganawa da Jekadan kasar China a Zauren Majalisar Dinkin Duniya. 路透社
Talla

Babbar Jaridar kasar China Peoples Daily ta wallafa matakin da kasar ta dauka na bin sahun kasar Rasha wajen bijerewa bukatar Majalisar Dinkin Duniya da ke neman kawo karshen mulkin Assad.

Sai dai Kasar Faransa tace kungiyar kasashen Turai zata karfafa takunkumin da suka sanyawa Syria,  tun da bukatarsu na daukar matsayi a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya samu cikas daga China da Rasha.

Tuni wannan mataki na kasashen Rasha da China, ya janyo suka daga kasashen Larabawa da Yammaci wadanda suka goyi bayan kudirin.

Kasashen Yammaci sun fusata, saboda sau biyu kenan a jere, aka kasa cim ma matsaya kan yadda Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya, zai taimaka wajen warware rikicin kasar ta Syria, inda ake zargin gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad da daukar tsauraran matakai akan masu zanga zanga, abunda ya kai ga mutuwan dubbai.

Rasha da China sun ce kudirin bai yi la’akari da bangarorin ba, kuma Rasha ta fusata ne dangane da yadda aka yi watsi da daftarin data gabatar tunda fari.

Masu rajin kare hakkin bil Adama na ganin rashin matsayar kasashen duniya, wata dam ace ga Shugaba Assad ci gaba da gallazawa Siriyawa masu adawa da gwamnatinsa.

Akwai rohotanni da ke cewa an kai wa ofisoshin jakadanci Syria bakwai hare hare domin nuna fushi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.