Isa ga babban shafi
Thailand-Combodia

Rikicin kan iyaka tsakanin Thailand da Combodia

Dakarun kasashen Cambodia da Thailand sunyi musayar wuta tsakaninsu a yau Litini a kwanaki hudu na yaki kan iyakar kasashen biyu, al’amarin ya janyo mutuwar akalla mutane shida. Tuni kasashen duniya suka nemi a kawo karshen rikicin.Babban sakataren Majalisar Dunkin Duniya, Ban Ki-moon ya nemi sassan biyu su tsagaita wuta, tare da nuna bakin ciki bisa faruwan lamarin. Kasar China tana cikin masu wannan kira na neman kawo karshen kai ruwa tsakanin kasashen na Cambodia da Thailand masu makwabtaka da juna, inda zaman zullumi ke karuwa.Dubban mutane a kauyukan dake kan iyakar kasashen sun kaura, sanadiyar sabon fadan da ya barke.Sabon rikicin wanda ya barke ya samo asali ne lokacin da Cambodia, wadda ta zargi Thailand da lalata wani wajen bauta, da aka gina a karni na 11.Tun cikin watan Yulin shekara ta 2008 ake samun zaman zullumi kan iyakar kasashen na Thailand da Cambodia. 

Wasu mazauna yankin da suka kaura kusa da wani wurin ibada  Preah Vihear
Wasu mazauna yankin da suka kaura kusa da wani wurin ibada Preah Vihear Reuters/Khem Sovannara
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.