Isa ga babban shafi
Thailand

Sarkin kasar ya nada babban habsan soja

A yau Alhamis Sarki kasar Thailand ya amince da nada wani janar din soja da ya jagoranci tarwatsa zanga zangar kin jinin gwamnatin da ta wakana a kasar, domin ya shugabanci rundunar sojan kasar, kamar yadda majiyoyin hukumar kasar suka tabbatar.A dazu ne Sarki Bhumibol Adulyadej ya sanya hannun kan tabbatar da nadin Janar Prayut Chan O Cha akan mukamin, domin maye gurbin Anupong Paojinda, a karkashin takande da rairaye da aka yi wa manyan hafsoshin sojan kasar ta Thailand 550.Prime Minista Abhisit Vejjajiva ya bayyana fatar ganin garambawul wa rundinar sojan kasar, domin tunkarar masu zanga zanga dake yawanta fitowa kan tituna, abunda ya janyo kafa dokar ta baci a Bangkok babban birnin kasar da wasu yanuka shida. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.