Isa ga babban shafi

Ƴan kasuwa a Uganda sun tsunduma yajin aikin ƙalubalantar ƙarin haraji

Harkokin kasuwanci sun tsaya cik a wasu manyan biranen Uganda, sakamakon yajin aiki kan adawa da matakin gwamnatin ƙasar na ƙarin haraji da kuma sabon tsarin ƙarbansa.

Ƴan kasuwar na Uganda na kalubalantar matakin shugaba Yoweri Museveni ne na zamanantar da tsarin karbar harajin dama kara yawan kudin da ake karba.
Ƴan kasuwar na Uganda na kalubalantar matakin shugaba Yoweri Museveni ne na zamanantar da tsarin karbar harajin dama kara yawan kudin da ake karba. © StateHouseUganda
Talla

Yajin aikin da kungiyar ƴan kasuwar Uganda ta kira na mambobinta su kauracewa wuraren sana’o’insu ya bazu daga babban birinin ƙasar Kampala zuwa wasu yankunan kasar a wannan Laraba, inda ƴan kasuwa suka rufe shaguna da sauran wuraren sana’o’insu domin biyayya ga uwar ƙungiyar da ta bukaci gwamnati ta janye ƙarin haraji da kuma salon biyansa.

Shugaban ƙungiyar FUTA John Kabanda ya ce hakan wani mataki na sai baba ta gani, don matsawa gwamnati lamba har sai ta saurare su.

Yanzu haka manyan shaguna da sauran sana’o’i kamarsu gidajen burodi da na abinci da mayanka sun kasance a killace a akasarin manyan biranen kasar ta Uganda.

Ƙungiyar ƴan kasuwar na adawa ne da matakin gwamnatin shugaba Yoweri Museveni na ƙarin haraji, har da na VAT kan kayan masarufi zuwa kaso 18 cikin ɗari, dai dai lokacin da babban bankin kasar ya yi karin ƙudin ruwa.

Wani batu da ya ƙara fusata ƴan kasuwar shi ne, sabon tsarin gwamnati wajen zamanantar da karban harajin ta hanyar na’ura mai ƙwaƙwalwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.