Kisan wani dan siyasar yankin Oromio a Habasha ya haifar da wani babban gibi
Kisan da aka yi wa wani babban dan siyasa na kungiyar ‘yan tawayen Oromio a kasar Habasha, ya haifar da zanga-zanga, kuma mai yiwuwa ya kara ta’azzara tashe-tashen hankula a yankin Oromia, mafi girma kuma mai mafi yawan jama’a a kasar.
Wallafawa ranar:
A wani bangare guda kuma, dukkaning bangarorin sun amince da cewa mutuwarsa babban rashi ne ga kasar Habasha.
A baya can dama Al'ummar Oromo sun yi dandazon murnar dawowar kungiyar 'yan adawa ta Oromo Liberation Front OLF da aka haramtawa gwamnati a baya, a dandalin Mesquel da ke Addis Ababa na kasar Habasha, a ranar 15 ga Satumba, 2018.
An harbe Bate Urgessa ne a wani wuri da ba a sani ba inda daga bisani aka tsinci gawarsa washegari a gefen wata hanya da ke wajen garin Meki da ke kudancin Addis Ababa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu