Isa ga babban shafi

Rasha ta tura dakaru zuwa Nijar domin bawa sojojin kasar horo

Wata tawagar dakarun sojin Rasha da manyan jami’ai daga ma’aikatar tsaron kasar sun isa Jamhuriyar Nijar domin horas da sojojin kasar, a wani yanayi da ke alamta cewa kasar da ke yammacin Afirka na kokarin kara kulla alaka da Moscow kamar sauran kasashe makwabta da ke karkashin mulkin soja.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da cimma wata yarjejeniyar habaka kawancen tsaro tsakanin sojojin da ke mulkin Nijar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da cimma wata yarjejeniyar habaka kawancen tsaro tsakanin sojojin da ke mulkin Nijar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. © AP
Talla

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan da cimma wata yarjejeniyar habaka kawancen tsaro tsakanin sojojin da ke mulkin Nijar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Tun a ranar Larabar da ta gabata ne wani gidan Talabijin na Nijar ya haska Dakarun sojin na Rasha a Yamai, babban birnin kasar, suna sauke kaya daga wani jirgin dakon kaya.

Kawo yanzu dai babu wani bayani daga kasar ta Rasha wadda a yanzu ke neman habaka tasirinta a Nahiyar Afirka, tare da tallata kanta a matsayin kawa ba wadda ta yi mulkin mallaka a Nahiyar ba.

Tun bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Dimokaradiya a shekarar da ta gabata, Nijar ta soke dadaddiyar alakar diflomasiyya da tsaron da ke Faransa, tare da karkata akalarta ga Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.