Isa ga babban shafi

Harin roka ya kashe sojojin Tanzania 3 a Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo

Wata roka da aka harba a gabashin Jamhuriyar Dimokaraɗiyar Congo ya yi sanadin mutuwar sojojin Tazania 3, wadanda ke daga cikin dakarun kiyaye zaman lafiya na yankin kudancin Afrika da aka aaka tura ƙasar don taimaka wa sojojinta yaƙi da mayaka ƙungiyar ‘yan tawayen M23.

Wasu sojojin rundunar yankin kudancin Afrika a Congo.
Wasu sojojin rundunar yankin kudancin Afrika a Congo. REUTERS - ARLETTE BASHIZI
Talla

Rundunar sojin ƙasashen yankin kudancin Afrika ta tura sojoji arewacin Kivu a watan Disamban shekarar da ta wuce don kama wa dakarun Congo a yakin da suke da M23.

Rundunar ta ƙunshi sojoji daga Afrika ta Kudu, Tanzania da Malawi.

Rundunar ta bayyana a wata sanarwa cewa  lamarin ya auku ne bayan da rikar da aka harba ta faɗi a kusa da sansanin da sojojin ke zama.

Sanarwar ta ƙara da cewa wani soja ɗan ƙasar Afrika ta Kudu ya mutu a asibiti a yayin da ake masa magani daga raunukan da yaa samu.

Bayan da suka shafe shekaru da dama ba tare da sun tada hankali ba, ‘yan tawayen M23, waɗanda akasarinsu ‘yan ƙabilar Tutsi ne, sun sake ɗaukar makamai  a shekarar 2021, kuma tun daga wannan lokaci sun kwace wasu yankuna a arewacin Kivu.

Jamhuriyar Dimokaraɗiyar Congo, Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen yammacin Turai suna zargin  Rwanda da bai wa ‘yan tawayen goyon bayaa a ƙoƙarinsu na karɓe yankin mai  ɗimbim albarkatun ƙasa, zargin da Rwanda ta musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.