Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya 6 sun mutu sakamakon harin mayakan Boko Haram

Akalla sojojin Najeriya 6 ne suka rasa rayukan su a wani harin kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka kai musu a kan hanyar Biu zuwa Buni Yadi, da ke jihar Borno.

Sojoji 6 ne suka mutu a sanadin harin
Sojoji 6 ne suka mutu a sanadin harin Getty Images
Talla

Mutuwar sojoji na zuwa ne kwanaki 7 dai-dai bayan binne sojoji 17 da wasu tsageru suka hallaka a jihar Delta, lamarin da ya tashi hankalin rundunar sojin kasar.

Jaridun kasar sun ruwaito cewa mayakan sun farwa sojojin a kauyen Kamuya dake gab da garin Buratai dake zaman mahaifar tsohon Hafsan tsaron kasar Laftanar Kanar Tukur Buratai.

Wata Majiya ta shaidawa manema labarai cewa sojojin sun gamu da ajalin su ne a lokacin da suka tsaya don shan mai a daya daga cikin gidajen mai dake kan hanya.

A baya-bayan nan sojojin Najeriya na gamuwa da ajalin su hannun ‘yan ta’adda lamarin da ke kara jefa tsaron kasar cikin hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.