Isa ga babban shafi

Lokaci yayi da Faransa zata kyautata kawancenta da Afrika- Ministan wajen Faransa

Faransa ta sha alwashin dai-daita alakarta da kasashen Afrika a kokarin da take yi na kafa sabon kawance da kowanne bangare zai amfana, sabanin alakar da ke a baya wadda ke amfanar bangare daya.

Ministan harkokin wajen Faransa Stephen Sejourne, yayin ziyara sa a Kenya
Ministan harkokin wajen Faransa Stephen Sejourne, yayin ziyara sa a Kenya AFP - SIMON MAINA
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Stephene Sejourne ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai kasar Kenya.

Wannan na zuwa ne bayan da alaka ke kara tabarbarewa tsakanin Faransa da wasu kasashen Afrika musamman wadanda ta yiwa mulkin mallaka a baya.

A yanzu dai a iya cewa Nahiyar Afrika ta zama wani filin yakin nuna kwarewar iya alaka tsakanin kasashen Turai, Amurka da kuma Rasha, inda wasu ke ganin wannan alkawari na Faransa na da alaka ta kai tsaye da yadda kasar taga Rasha na kara samun tasiri a Afrika.

Da yake nasa jawabin yayin karbar bakon, Ministan harkokin wajen Kenya Musalia Mudavadi ya ce dama babban abinda Afrika ke bukata a yanzu shine alakar da zata amfanar da kowanne bangare ba wai nuna isa daga wata kasa ko kuma karfin iko ba.

Ya ce duk da matukar muhimmanci da Afrika ke da shi ga Faransa ya dace kasar ta fahimci cewa mutane ne suke rayuwa a yankin kuma suna da ikon tsarawa kansu yadda zasu tafiyar da harkokin yau da kullum ba tare da katsalandan ko kuna karfin iko daga wata kasa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.