Isa ga babban shafi

Dubban ‘yan Morocco sun gudanar da zanga-zangar kin jinin Isra’ila

Dubban ‘yan Morocco a babban birnin kasar Casablanca, sun gudanar da zanga-zangar yin A wadai da Isra’ila kan kisan kiyashin da take yi wa Falasdinawa a Zirin Gaza.

'yan Morocco na zanga-zangar kin amincewa da Isra'Ila
'yan Morocco na zanga-zangar kin amincewa da Isra'Ila REUTERS - STRINGER
Talla

Masu zanga-zangar sun kuma yi amfani da damar wajen neman gwamnatin kasar ta Morocco ta soke alakar Diflomasiyar da ta maida tsakaninta ta Isra’ila a shekaru uku da suka gabata.

Kungiyar Al Adl Wal Ihssan da gwamnati ta haramta ayyukanta ce ta kira zanga-zangar wadda itace irinta mafi girma da aka gani a Morocco.

Bayanai sun kuma ce an gudanar da zanga-zangar kin jinin ta Isra’ila a biranen rabat da kuma Tangier.

A karshen shekarar 2020 Morocco ta gyara alakarta da Isra’illa a karkkashin shiga tsakanin Amurka da ya samu nasarar daidaita Isra’ilar da karin kasashen da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain.

Bayan sulhun ne kuma Amurka ta marawa gwamnatin kasar ta Morocco baya dangane da ikirarinta na cikakken iko yankin Yammacin Sahara da ta kwashe shekaru tana rikici da ‘yan tawayen Polisario a kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.