Isa ga babban shafi
RIKICIN ISRA'ILA DA HAMAS

Yahudawa na zanga-zangar adawa da Netanyahu a Birnin Kudus

Zanga-zangar adawa da gwamnatin Benjamin Netanyahu na neman sauyawa zuwa tashin hankali a Birnin Kudus yayin da majalisar ministocin Firaministan ke fuskantar suka kan harin da Hamas ta kai Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba.

Yadda Yahudawa ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Netanyahu a birnin Kudus kenan.
Yadda Yahudawa ke zanga-zangar adawa da gwamnatin Netanyahu a birnin Kudus kenan. © Leo Correa / AP
Talla

An kuma yi arangama a unguwar Mea Shearim tsakanin Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi da kuma dakarun soji.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda ke murmurewa daga tiyatar da aka masa, na fuskantar matsalolin siyasa, yayin da masu zanga-zangar ke kira da a gudanar da sabon zabe cikin gaggawa, da kuma yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin kubutar da sauran wadanda aka yi garkuwa da su.

A halin da ake ciki kuma sojojin Isra'ila sun janye daga asibitin al-Shifa bayan wani samame na makonni 2 da suka kai.

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce majiyyata 21 ne suka mutu sakamakon mamayar da dakarun na Isra’ila suka kaddamar a wannan yanki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.