Isa ga babban shafi

Harin masu dauke da makamai ya kashe mutum 73 a Burkina Faso

Akalla mutane 73 ne aka kashe a Tawori da ke gabashin Burkina Faso, sakamakon harin mayakan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Jnim da ke goyon bayan kungiyar Al-Qaeda.

Yadda aka gudanar da jana'izar sojoji bakwai da masu dauake da makamai suka kashe a gabashin Burkina Faso ranar 31 ga Agusta, 2018.
Yadda aka gudanar da jana'izar sojoji bakwai da masu dauake da makamai suka kashe a gabashin Burkina Faso ranar 31 ga Agusta, 2018. AFP
Talla

Daga cikin wadanda abin ya shafa, akwai fararen hula 32 tare da sojoji 16 da kuma mayakan sa kai 25 da ke kokarin kare kasar daga masu ayyukan ta’addanci.

A cewar bayanan da RFI ta gano, maharan dauke da Babura 200 sun kai hari kan sojojin da ke tsaka da aiki, inda suka yi nasarar kwace sansanin su da kuma makaman yaki.

Akwai adadin sojojin da har yanzu ba a san inda suke ba, ko da yake bayanai sun nuna cewa mayakan sun yi awun gaba da sojoji biyu a matsayin fursunan yaki.

Tuni dai kungiyar masu tsatssauran ra’ayin ta Jnim ta dauki alhakin kai harin tare da fitar da wani faifan bidiyon sojojin biyu a shafukan sada zumunta.

Gwamnatin sojin Burkina Faso, karkashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traore, wadda ta tabbatar da faruwar hakan, ta ce ta daura damarar sabon salon yaki da ayyukan masu tayar da kayar baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.