Isa ga babban shafi

Benin da Nijar sun cimma yarjejeniyar saukakawa 'yan kasuwa kudin fiton kayayaki

Gwanatin Jamhuriyar Benin, ta ce za ta yiwa 'yan kasuwar Nijar ragin daga kaso 40 zuwa 50 bisa 100 na kudin fiton kayayyakin da ake karba a hannun su, amma na kayayyakin da suka shafe tsawon watanni jibge a tashar ruwan Cotonou.

Jiragen ruwa kenan da aka ajiye a tashar jiragen ruwa Cotonou da ke Jamhuriyar Benin.
Jiragen ruwa kenan da aka ajiye a tashar jiragen ruwa Cotonou da ke Jamhuriyar Benin. © Prospoer Dagnitche / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne, yayin da dangantaka ta yi tsami tsakanin kasashen biyu, sakamakon rufe iyakar da Benin tayi tsakaninta da Nijar, biyo bayan takunkumin da ECOWAS ta kakabawa kasar.

Tun farko dai ECOWAS ta kakabawa Nijar din takunkumin tattalin arziki ne, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yiwa zababben shugaban Kasar Mouhammad Bazoum a shekarar 2023.

Sai dai a ta bakin sakataren kungiyar 'yan kasuwar da ke shige da ficen kayayyaki a Jamhuriyar Nijar, Chaibou Tchiombiano ya ce tuni suka cimma yarjejeniya da hukumomin tashar ruwan Cotonou da kuma hukumar kula da harkokin Sulfurique ta Nijar din.

Shiga alamar sauti, domin sauraron hirar sa da RFI.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.