Isa ga babban shafi

Mutum biyu sun jikkata a wani sabon harin kunar bakin wake a Borno

Rundinar ‘yan sanda a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta tabbatar ta mutuwar wani dan kunar bakin wake tare da jikkata mutum biyu a karamar hukumar ta jihar a jiya Lahadi.

Hoto don misali.
Hoto don misali. © Réseaux sociaux
Talla

Kakakin rundinar ASP Daso Nuhum ne ya tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin.

Ya ce dan kunar bakin waken ya kashe kansa ne a lokacin da ya yi yunkurin kutsawa cikin masallata a lokacin da suke tsaka da sallar Tarawihi da misalin karfe 8 na daren jiya a cikin garin Biu, inda ya jikkata mutane biyu.

Rundinar ‘yan sandan jihar ta yi kira ga jama’a da su kara sanya ido musamman cikin wannan wata na azumin Ramadana da al’ummar musulmi ke fita sallar dare tare da sanar da hukumomin tsaro da zarar sun ga wani abu da basu aminta da shi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.