Isa ga babban shafi

Hukumar Kwastam ta kama harsasan da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 a cikin buhunan garin rogo

Hukumar Kwastam reshen jihar Ogun, ta ce ta kama tarin harsasai 940 da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 a yankin Idiroko, a boye a cikin buhunan garin rogo.Shugaban Hukumar Kwastam a yankin, Ahmadu Shuaibu, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Juma’a a Idiroko, Ogun.

Kwantrollan Kwastam  Uba Mohammed Garba
Kwantrollan Kwastam Uba Mohammed Garba RFI Hausa
Talla

Hukumar da ta samu bayyanai dangane da batun safarar mutane a yayin da ake bin sahun ‘yan fashin, bayanan sirri sun nuna irin yadda ake sa ido kan wasu mutanen daban da ake kyautata zaton suna shigo da makamai da safarar mutane daga jamhuriyar Benin zuwa  Najeriya.

Lokacin da ake kone tarin kayaki a Seme
Lokacin da ake kone tarin kayaki a Seme RFI Hausa

 Jami’in ya bayyana cewa an kama kayayyakin ne a magudanar ruwa, layukan kan iyaka da sauran muhimman wurare a fadin jihar ta Ogun, ta hanyar hukumar leken asiri ta rundunar da kuma ayyukan sintiri na sa’o’i 24 na jami’an hukumar kwastam.

Yan Sanda sun taimaka wajen samun nasarar wannan aiki,yayin wannan ganawa da manema labarai,hukumar ta kwastam ta bayyana cewa ta kama buhu 123 da kwalaye 3,172 na tabar wiwi, da wasu tarin kayaki da suka hada da fatu,tufafi, kwalaye 910 na daskararrun kayayyakin kiwon kaji da dai sauransu.

wasu daga cikin albarusan yaki da aka shigo da su ta bayan fage
wasu daga cikin albarusan yaki da aka shigo da su ta bayan fage (Photo : Laurent Correau)

Shugaban hukumar ta Kwastam a yankin ya kiyasta kamu wadanan kayaki da kusan kudi naira miliyan 557.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.