Isa ga babban shafi

Rundunar sojojin Najeriya na farautar wadanda suka kashe jami'anta 16 a Delta

Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta sha alwashin ganin ta farauto matasan da ake zargi da kashe jami’an sojoji 16, wanda ke aiki a karkashin bataliya ta 181 a karamar hukumar Bomadi ta Jahar Delta.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. © Sawaba Radio
Talla

A cikin sanarwar da daraktan yada labarai na shalkwatar tsaron kasar Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, ta ce matasan da ke dauke da makamai, sun yi wa jami’an sojojin kawanya ne sannan suka kashesu.

Babban jami’in rundunar sojin ya ce daga cikin wadanda ‘yan ta’addan suka kashe, harda kwamandan da ke jagorantar sojojin da wasu masu mukanin Manjo biyu da wani mai mukamin kyaftin daya sai kuma kananan sojoji 12 da suke aikin samar da zaman lafiya a yanki.

A cewarsa babban hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa, ya bada umarnin fara gudanar da bincike kan lamarin da tuni aka samar da gwamnatin Jahar ta Delta faruwansa, tare kuma kamo wadanda suka aikta laifin.

“Ya zuwa yanzu, an samu nasarar kama wasu yayin da ake daukar matakai domin bankado makasudin kai harin.”

Rahotanni sun nuna cewar lamarin ya faru ne a ranar Alhamis din da ta gabata, bayan da aka yi wa sojojin kiran gaggawa don su kawo dauki kan rikicin da aka samu tsakanin kauyukan Okuoma da kuma Okoloba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.