Isa ga babban shafi

Sojojin Najeriya sun dakile hare-haren Boko Haram a Kano

Wani samamen hadin gwiwa da aka yi tsakanin rundunar sojojin Najeriya da kuma hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ya dakatar da shirin kai wani mummunan harin da ‘yan tada kayar baya ke shirin kai wa a jahar Kano.

Sojojin Najeriya dake yakar kungiyar Boko Haram
Sojojin Najeriya dake yakar kungiyar Boko Haram STEFAN HEUNIS / AFP
Talla

A cewar daraktan yada labarai na rundunar sojojin Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, a ranar juma’ar nan ce suka kai samame a maboyar ‘yan ta’addan da ke karamar hukumar Gezawa.

Ya ce sun kai harin ne da zummar bankado tare da kama wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, wandan da ke shirin kai wasu hare-haren a jahar Kano.

Janar Nwachukwu ya ce jami’ansu da ke aiki karkashin Birget ta 3, sun samu nasarar kama mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin, sannan sun gano bindigu kirar AK-47 da alburusai da makamin roka da ababen faashewa 5 da sinadaren hada  ababen fashewa da kuma kakin jami’an tsaro.

“Hadin kai tsakanin rundunar sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro kamar yadda aka yi misali da su wajen gudanar da aiki, shaida ce ta karfin kudirin mu na murkushe ‘yan ta’adda da sauran matsalolin tsaro. Wannan samame da aka samu nasara yana kara karfafa jajircewar sojojin Najeriya na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa”.

Onyema ya kara da cewar rundunar sojojin Najeriya, na nan kan bakarta wajen yaki da ‘yan ta’adda da duk wasu masu kawo wa tsaron kasar barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.