Majalisar dokokin Togo ta fara muhawwara kan gyarar kundin tsarin mulkin kasar
Majalisar dokokin Togo ta fara mahawara a game da wani daftari da ke neman yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kuma matukar aka amince da gyarar, hakan zai sauya salo a game da yadda ake zaben shugaban kasa da kuma adadin shekarun da zai share kan karagar mulki.
Wallafawa ranar:
Idan dai har majalisar ta amince da wannan sauyi, to hakan na nufin cewa Togo za ta daina amfani da tsarin shugaban kasa da da al’umma ke zabe kai-tsaye zuwa wanda ‘yan majalisar dokoki zabe.
Har ila yau daftarin ya ce za a zabi shugaban kasa domin yin wa’adin mulki na tsawon shekaru 7 har sau biyu, sabanin kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi a yau da ake zaben shugaba tsawon shekaru 5 kacal.
Wani sauyi a cikin sabon daftarin shi ne, majalisa ce za ta rika nada firaminista da za a kira shi da suna shugaban gwamnati. Kundin tsari mulkin da kasar ke amfani da shi yanzu haka an kirkire shi ne tun 1992, to amma an yi masa gyare-gyare sau da dama, kuma na karshe shi ne wanda aka yi a 1999, kuma a karkashinsa, ana zaben shugaban kasa wa’adin shekaru 5 ne tare da damar sake tsayawa karo na biyu kawai.
To sai dai kungiyoyin da ke fafutuka domin tabbatar da dimokuradiyya a Togo, na ganin cewa ‘yan majalisar dokokin kasar ba su da hurumin zaunawa balantana yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, domin kuwa wa’adin da aka zabe su a kai, ya kawo karshe tun a watan disambar da ya gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu