'Yar Senegal ta lashe kyautar Golden Bear
‘Yar kasar Senegal Mati Diop ta lashe kyautar girmamawa ta ‘Golden Bear’ yayin bikin bajakolin nuna fina-finai da aka saba yi a birnin Berlin.
Wallafawa ranar:
Diop ta lashe kyautar ce da fim din da ta shirya kan gwagwarmayar dawo da kayayyakin tarihin da turawan mulkin mallaka suka sace a nahiyar Afrika.
Wannan shi ne karo na biyu da wani Shirin fim daga nahiyar Africa ya samu nasarar lashe irin wannan kyauta mai daraja.
Fim din mai suna Dahomey, ya duba yadda a shekarar 2021 kasashen Jamus, Faransa da Belgium suka jagoranci maido da kayayyakin tarihi 26 da Faransa ta sace a zamanin mulkin mallaka na tsohuwar daular Dahomey wato kasar Benin.
Wani dan jarida kuma mai sharhin fina-finai a Senegal Baba Diop, ya bayyana nasarar matashiyar a matsayin kwarin gwiwa ga matasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu