Isa ga babban shafi

An kammala bikin baje kolin fina-finai na Cannes karo na 75 a Faransa

An kammala bikin baje kolin fina-finai karo na 75 a karshen mako, wanda aka gudanar a  Kudancin Faransa, yayin da aka karrama wasu taurari da lambobin yabo.

Alkalan bukin baje kolin fina-fina na Cannes karo na 75
Alkalan bukin baje kolin fina-fina na Cannes karo na 75 © LOIC VENANCE / AFP
Talla

Fitaccen mai shirya fina-finai dan asalin Sweden, wato Ruben Ostlund ya lashe babbar kyautar Palme d’Or saboda basirar da ya zuba a cikin fim dinsa na Triangle of Sadness.

Sai kuma kyauta ta biyu mafi girma ta Grand Prix, wadda a bana, aka bai wa Lukas Dhont na Belgium saboda bajintar da ya nuna wajen bada umarni a fim dinsa na Close, yayin da ita ma Claire Denis ta Faransa ta karbi makamanciyar wannan kyauta a dalilin fim dinta na Stars Noon da ta bada umarni.

Kyautar darekta mafi kwarewa, an  mika ta ne ga Park Chan-wook na Korea ta Kudu da ya shirya fim din Decision to Leave, yayin da a bangaren mata, Zar Amir Ebrahimi ta Denmark, ta lashe makamanciyar wannan kyuata saboda fim dinta na Holy Spider.

Har wa yau, shi ma Song Kang-ho na Korea ta Kudu ya samu kyautar ta darekta mafi kwarewa a dalilin fim dinsa na Broker.

A game da basirar rubuta shirin fina-finai kuwa, Tarik Saleh na Sweden ne ya lashe kyautar saboda fim Boy from Heaven da ya rubuta.

An dai bada sauran kananan kyautuka da suka hada da ta wadda ya fi iya daukar hoto kuma wasu Amurkawa biyu ne suka lashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.