Isa ga babban shafi

Kungiyoyin masu dauke da makamai a Libya sun amince su fice daga birnin Tripoli

Kungiyoyi masu dauke da makamai da ke rike da ikon birnin Tripoli fiye da shekaru goma sun amince za su kwashe kayansu daga babban birnin na kasar ta Libiya.

Kasar ta jima tana fama da matsalar masu dauke da makamai
Kasar ta jima tana fama da matsalar masu dauke da makamai © AFP
Talla

Ministan cikin gidan kasar Imad Trabelsi, ne ya bayyana hakan bayan tattaunawa mai tsawo kan kulla yarjejeniya da dakarun.

Yarjejeniyar dai na zuwa ne bayan wani kazamin fada da aka yi a birnin cikin watannin baya-bayan nan.

Kasar ta Libya dai ta sha fama da kungiyoyi masu dauke da makamai da dama wadanda suka bayyana bayan hambarar da gwamnatin Muhammad Gaddafi a shekarar 2011.

Tashe-tashen hankula da suka yi sanadiyar kashe shugaban kasar na tsawon lokaci ya haifar da tabarbarewar tsaro, inda tun lokacin kasar ke fama da rikice-rikice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.