Isa ga babban shafi

Birtaniya ta tallafawa Africa da sama da fam miliyan 300 a bara kadai don yaki da ta'addanci

Gwamnatin Burtaniya ta kashe zunzurutun kudi har fan miliyan 300 wajen gudanar da shirye-shiryen inganta tsaro a Nahiyar Africa a bara kadai da nufin ciyar da yankin gaba.

Tutar kasar Burtaniya
Tutar kasar Burtaniya AFP
Talla

Karamin ministan harkokin wajen Amurka Baroness Lucy ne ya bayyana hakan, a wata ziyara da ya kai Najeriya da nufin sake karfafa alakar da ke tsakanin su.

Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar kasashe rainon Ingila da ke Ofishinta na Najeriya Atinuke Akande-Alegbe ya fitar, ta ce wannan ziyara ta zo ne a  dai-dai lokacin da Najeriya ke bukatar ta, duba da irin matsalolin da suka dabaibaye kasar.

Ziyarar ministan na zuwa ne kwanaki biyu bayan taron hafsoshin tsaro da kasashen biyu suka gudanar, inda kuma suka amince da musayar bayanan sirri kan harkokin tsaro ta kan yanar gizo, baya ga amincewa da aiki tare a fannin habbaka doka da oda da kuma kare hakkin dan adam.Yayin da kasashen biyu ke aiki tare wajen bankado masu laifi, sanarwar ta ce jami’an tsaron hadin gwiwa na kasashen biyu sun gano tan 3 na haramtattun kwayoyi da ake safarar su tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma kasashen biyu sun yi hadin gwiwa wajen tallafawa mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallan su a yankin arewa maso gabashin Najeriya.Rikicin dai ya raba mutane fiye da miliyan 11 a tsakanin kasahen Najeriya, Kamaru Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar da muhallan su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.