Isa ga babban shafi

Shugaban kasar Mauritania ya zama sabon shugaban kungiyar tarayyar Afirka

Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ghazouani ya zama sabon shugaban kungiyar tarayyar Africa ta AU.

Shugaban kasar Mauritania Mohamed Ghazouani
Le président mauritanien en novembre 2022. AFP - BANDAR AL-JALOUD
Talla

Yayin taron shugabannin kungiyar karo na 37 a birnin Adis Ababa, Ghazouani ya sami nasara a kwarya-kwaryan zaben da aka gudanar.

Mr Mohamed ya karbi shugabancin hukumar daga hannun Azali Assoumani na kasar Comoros, wanda ya jagorance ta a 2023.

Da alama kungiyar ta kaucewa rikici da rarrabuwar kawuna da ka iya tashi sakamakon shirya cikakken zabe, don haka aka yi amfani da tsarin karba-karba wajen mika mulkin zuwa ga kasar Maurtania da ke wakiltar yankin gabashin Africa.

Kasashen Morocco da Algeria sun jima suna gwagwarmayar samun shugabancin hukumar, yayin da suke kalubalantar salon shugabancin hukumar da ke karbar umarni kai tsaye da turawa ba tare da la’akari da matsalolin cikin gida a Africa ba.

Mohamed Ghazouani zai jagoranci hukumar na tsahon shekara guda kafin ya sake sauya hannu zuwa wani sashen na Africa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.