Isa ga babban shafi

Ruwan karkashin kasa na tayar da hankalin jama’a a kasar Libya

A garin Zliten da ke yammacin kasar Libya,jama’a na rayuwa cikin fargaba ganin ta yada ruwan karkashin kasa suka tilastawa iyalai da dama tserewa daga gidajensu da a baya ambaliyar ruwa ta lalata, babar dammuwa ita ce ta bangaren muhalli kamar dai yada hukumomin suka sanar.

Birnin Derna a watan Satumba
Birnin Derna a watan Satumba AFP - -
Talla

A watan satumba da ya gabata ne mumunan ambaliyar ruwa ta lalata garin Derna da ke gabashin kasar, a wani sabon rahoto Zliten mai tazarar kilomita 160 daga Tripoli babban birnin kasar a cewar mazauna garin da aka kiyasta yawansu da kusan 350,000, lamarin ba sabon abu bane a wannan yanki musaman hawan ruwan karkashin kasa amma girmansa a halin yanzu ba a taba ganin irinsa ba. Gidaje da dama, tituna da gonaki sun cika makil da ruwa.

Jama’a sun soma fuskanatar wannan matsalla watanni biyu da suka gabata,yayinda al’amarin ke ci gaba inda a wasu yankuna ,ruwan suka mammaye rijiyoyi.

Makarantar horar da yan Sanda a birnin Zliten
Makarantar horar da yan Sanda a birnin Zliten REUTERS/Stringer

Iyalai suna fargabar cewa lamarin zai kara ta'azzara, suna barin gidajensu cike da ruwa, a wasu unguwani gidaje sun soma rushewa.

Bugu da kari, ruwa da laka a kan tituna da itatuwan dabino a wasu wuraren inda jama’a ke iya kokarin ganin sun canza wurin zama.

Tsakiyar birnin Derna
Tsakiyar birnin Derna © Houda Ibrahim/RFI

Moftah Hamadi magajin garin ya ce hukumomin suns amar da wani tsari na tallafawa kusan iyalai hamsin wandada aka ba su damar kaura ko kuma aka basu kudi don su samu hayar masauki.

A yayin taron majalisar ministocin a ranar 6 ga Fabrairu, Firaminista Abdelhamid Dbeibah ya yi wa mazauna Zliten alkawarin cewa gwamnatinsa "ba za ta yi kasa a gwiwa ba" don kawo karshen wannan matsallar cikin gaggawa.

Ya bukaci ministocin da abin ya shafa da su dauki matakan da suka dace don biyan diyya ko tsugunar da iyalai da abin ya shafa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.