Isa ga babban shafi
AFCON

'Yan sandan Najeriya sun bayyana goyan bayan su ga Super Eagles

Najeriya – Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta aike da sakon fatan alheri ga tawagar kungiyar Super Eagles dake shirin karawa da takwarorin su na Cote d'Ivoire a gasar AFCON, inda take musu fatan alheri.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya
Tawagar Super Eagles ta Najeriya © AFCON 2023
Talla

A wani yanayin da ba'a saba gani ba,  kakakin rundunar ya gabatar ta bukaci zaratan 'yan wasan na Eagles da su ci gaba da fafutukar su wajen nuna wa Cote d'Ivoire banbancin dake tsakanin kasashen biyu a harkar kwallon kafa.

Rundunar tace kamar yadda hotan mikiyar dake alama rundunar su, ya dace kungiyar ta Super Eagles ta yi shawagi a sama wajen nuna fifikon dake tsakanin su da Cote d'Ivoire wanda ake yiwa lakabi da giwaye.

Sufeto Janar Kayode Egbetokun
Sufeto Janar Kayode Egbetokun © Nigeria Police

Sufeto Janar na 'Yan Sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bukaci 'yan wasan Najeriya da su cirewa kasar kitse a wuta wajen dauko kofin domin dawo da shi Najeriya.

Samun nasarar wannan karawar zai sanya Najeriya cikin jerin kasashen da suka fi yawan lashe gasar a Afirka.

Tuni tawagar 'yan siyasa da shugabannin hukumomin gwamnatin Najeriya tare da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima suka isa Abidjan domin marawa 'yan wasan najeriya baya a karawar ta daren yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.