Isa ga babban shafi
GASAR AFCON

'Yan Afirka ta Kudu na barazanar kai wa 'yan Najeriya hari saboda Super Eagles

Najeriya – Gwamnatin Najeriya ta roki ‘yan kasar ta mazauna Afirka ta Kudu da su kaucewa bayyana farin cikin su a fili idan kungiyar Super Eagles ta samu nasara a kan Bafana Bafana a gasar cikin kofin Afirka dake gudana a Abidjan.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya da ta fafata da Guinea-Bissau.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya da ta fafata da Guinea-Bissau. © AFCON 2023
Talla

Gobe ne ake saran kasashen biyu su fafata domin samun tikitin zuwa wasan karshe na gasar dake ci gaba da dauke hankalin masu sha’awar kwallon kafa a kasashen duniya.

‘Yan Najeriya da dama dake zama a biranen Afirka ta Kudu sun bayyana samun sakonnin barazana daga wasu ‘yan kasar dangane da wannan wasa da za’ayi gobe laraba.

Daya daga cikin shugabannin ‘Yan Najeriyar mazauna kasar Godwin Okeke yace ba a yau suka fara fuskantar irin wannan barazana daga mutanen kasar ba, inda yace ko a shekarun baya da kungiyar kwallon kafa ta matar Najeriya ta je can domin karawa da takwarorinsu na Afirka ta kudu, su da magoya bayan su da kyar suka sha, sakamakon hare haren da aka kai musu da duwatsu saboda nasarar Najeriyar.

Ahmed Musa, kaften din tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles
Ahmed Musa, kaften din tawagar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles © RFI/ Abdurrahman Gambo

Sanarwar da ofishin jakadancin Najeriya dake Pretoria ya gabatar, ya bukaci ‘yan Najeriya suyi taka tsan tsan wajen kalaman su da kuma inda suke shiga domin kaucewa barazanar da wasu bata gari ke yi na kai musu hari.

Ofishin Jakadancin ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kaucewa bukukuwa idan kasar ta samu nasara, tare da kuma kira a gare su da su zama masu bin doka da oda a koda yaushe.

Magoya bayan tawagar Super Eagles ta Najeriya
Magoya bayan tawagar Super Eagles ta Najeriya AP - Sunday Alamba

‘Yan kasar Afirka ta Kudu sun dade suna kai munanan hare hare a kan ‘yan Najeriya da kuma wasu ‘yan Afirka saboda zargin da suke musu na mamaye harkokin kasuwanci da ayyukan yi, yayin da suke zargin bakin da kuma hada hadar kwaya.

A shekarar 2019 akalla baki 10 aka kashe a Afirka ta Kudu lokacin da wasu batagarin matasa suka dinga kai hari a kan ‘yan kasashen Afirka da kuma wuraren kasuwancin su, abinda ya tinzira shugaban kasa na lokacin Muhammadu Buhari janye jakadan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.