Isa ga babban shafi

Shugaban kasar Namibia Hage Geingob ya rasu yau Lahadi

Shugaban kasar Namibia Hage Geingob ya rasu da sanyin safiyar yau lahadi a wani asibiti a birnin Windhoek inda yake jinya bayan fama da cutar daji.Tsohon Shugaban kasar ,Hage Geingob, wanda ya kafa tarihin a fagen siyasar kasar ta Namibia a matsayin firaminista kuma ya shugabanci kasar ya kasance dan gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata kafin ya zama dan siyasa.

Hage Geingob, Shugaban kasar Namibia
Hage Geingob, Shugaban kasar Namibia Foreign and Commonwealth Office/wikimedia.org
Talla

Hage Geingob ya rasu ne da safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Windhoek babban birnin kasar, yana  da shekaru 82 a duniya.

An haifi Hage Gottfried Geingob a wani kauye da ke arewacin Namibia a shekara ta 1941, shi ne shugaban kasar farko na kudancin Afirka ba daga kabilar Ovambo ba, wadda ke da fiye da rabin al'ummar kasar.

Hage Geingob, Tsohon Shugaban Namibia
Hage Geingob, Tsohon Shugaban Namibia Foreign and Commonwealth Office/wikimedia.org

Ya kaddamar da yaki da mulkin wariyar launin fata na Afirka ta Kudu, wanda ya mulki Namibia a lokacin, tun daga farkon shekarunsa na karatu kafin a tilasta masa yin gudun hijira.Ya shafe kusan shekaru talatin a Botswana da Amurka.

Monica Geingos, Uwargindan Shugaban kasar Namibia
Monica Geingos, Uwargindan Shugaban kasar Namibia AFP - ISSOUF SANOGO

Gottfried Geingob ya yi karatu a Jami'ar Fordham da ke New York sannan ya sami digiri na uku a Birtaniya.A cikin shekarun da ya yi a Amurka, ya yi kaurin suna wajen kare 'yancin kai na Namibia, wanda ke wakiltar kungiyar 'yantar da 'yanci ta gida, SWAPO, wadda ita ce jam'iyya mai mulki a yau, a Majalisar Dinkin Duniya da ma daukacin nahiyar Amurka.

A farkon shekarun 1970, ya fara aiki da Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin mulki.

A tsakiya  Hage Geingob Shugaban kasar Namibia
A tsakiya Hage Geingob Shugaban kasar Namibia AFP PHOTO/JORDAANIA ANDIMA

Ana yi masa kallon mai kishin kasa, ya koma Namibia a shekarar 1989, shekara guda kafin kasar ta samu ‘yancin kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.