Isa ga babban shafi

Namibiya za ta sayar da kada sama da 40 domin rage yawansu a kasar

Kasar Namibiya ta yi shelar sayar da wasu kaduna guda 40 domin rage tashe-tashen hankulan da ake samu tsakanin mutane da namun daji a yankunan Kavango da Zambezi dake arewa maso gabashin kasar.

Hukumomin kasar sun ce yawan dabbar na ci gaba da kasancewa barazana ga jama'a.
Hukumomin kasar sun ce yawan dabbar na ci gaba da kasancewa barazana ga jama'a. © AFP
Talla

Ana sa ran masu sha'awar siyan dabbobin da ke rarrafe za su gabatar da tayin su a ma'aikatar muhalli daga nan zuwa ranar 17 ga watan gobe na Yuli.

Mai magana da yawun ma'aikatar Romeo Muyunda ya ce yawancin namun daji na kasar suna wuraren shakatawa na kasa, wanda ya sanya yankunan ke ci gaba da fuskantar hare-haren kada kan mutane da dabbobinsu.

Dole ne bukatar sayen kadar su tabbatar da cewa suna da wurin da ya dace da irin dabbobin kuma za su bayyana dalilan su na sayen su.

Masu neman fitar da su daga kasar kuwa, gwamnatin Namibiya ta ce, dole ne su gabatar da takardun izini daga kasashen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.