Isa ga babban shafi

Rumbun ajiyar makamai da ke Yimdi a Burkina Faso ya kama da wuta

A  Burkina Faso,babban hafsan sojin kasar a wata sanarwa da ya fitar ,ya nemi jama’a sun kwantar da hankulan su biyo bayan wasu fashe-fashe da aka ji sakamakon wata gobara da ta tashi a rumbun ajiyar makamai da ke Yimdi a kasar.

Dakarun Burkina Faso
Dakarun Burkina Faso © Issouf Sanogo, AFP
Talla

Ganin ta yada jita-jita ya yadu a kasar musaman a shafukan sada zumunta,takanas bayan 'yan sa'o'i ne, babban hafsan sojojin ya ba da cikakken bayani a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai.

Wani sojin Burkina Faso
Wani sojin Burkina Faso © ISSOUF SANOGO / AFP

Babban hafsan sojin kasar ya tabbatar da cewa an shawo kan gobarar cikin gaggawa sakamakon daukar matakin da jami’an kashe gobara suka yi. Rundunar sojojin wadda ba ta bayar da wani bayani kan barnar da gobarar ta haddasa ba, ta yi kira ga jama'a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.