Hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari ga Shugaban jam'iyyar Ennahdha
Kotun Tunisia ta yanke hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari ga Rached Ghannouchi, shugaban jam'iyyar Ennahdha, watanni goma bayan kama shi da aka yi a gidansa.Rached Ghannouchi ya kasance shugaban majalisar dokokin Tunisia zuwa lokacin da Shugaban Kaïs Saïed ya karbi mulki.
Wallafawa ranar:
Ana tuhumar Rached Ghannouchi da sunan jam’iyyar sa karbar kudaden daga kasashen Wanda ya sabawa dokokin kasar ta Tunisia.
‘yan lokuta da zartar da hukuncin, jam’iyyarsa ta yi watsi da zarge-zargen. Shugaban kasar na gudanar da mulkinsa ba tare da nuna tausayi ba.
Tsohon ministan harkokin wajen kasar Rafik Abdesselam, dan kungiyar Ennahdha kuma surukin Rached Ghannouchi, ya fuskanci irin wannan hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu