Isa ga babban shafi

An kama 'yan ta'addan da suka tsere daga gidan yari a Tunisia

Jami’an tsaro a Tunusia sun samu nasarar kama mutane biyar masu tsatsuran ra’ayin addini, da suka gudu daga gidan yarin da ake tsare da su a makon da ya gabata, bisa aikata laifin kashe wasu ‘yan siyasa biyu da kuma ‘yan sanda.

Shugaban Tunisia Kais Saied.
Shugaban Tunisia Kais Saied. AFP - FETHI BELAID
Talla

Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta ce, da sanyin safiyar Talatar nan ce aka kama mutane 4 daga cikinsu a tsuburin da ke kusa da birnin Tunis, sannan cikon na biyar din an kama shi kwanaki biyu da su ka gabata tare da taimakon jama’a.

Tserewar ta su daga gidan yari ya sanya gwamnatin kasar daukar matakin korar wasu manyan jami’an sirri, sakamakon sakacin da ake ganin an samu a sha’anin tsaro.

Hukumomin tsaro sun bayyana mutane a matsayin ‘yan ta’adda da ke da hatsari, domin daga cikinsu akwai Ahmed Malki da aka fi sani da Somali, wanda ya ke fuskantar daurin shekaru 24 bisa kashe ‘yan siyasa Chokri Belaid da kuma Mohamed Brahmi a shekarar 2013.

Tun bayan komawa mulkin dimukaradiya a shekarar 2011 a Tunisia, kungiyoyin masu ikirarin jihadi sun kashe ‘yan sanda da masu yawon shakatawa da dama a kasar, duk da cewar gwamnatin kasar ta yi nasarar kashe ko kama wasu manya da ke cikinsu a ‘yan shekarun nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.