Tawagogi 50 daga Afirka zasu halarci taron birnin Roma kan batun bakin haure
A yau ake soma taron birnin Roma na kasar Italiya da Afrika,tawagogi 50 daga kasashen Afirka zasu kasance a birnin na Roma. Shugabannin kasashen Turai da wakilan kungiyoyin kasa da kasa kuma za su halarci taron,inda gwamnatin Italiya ke shirin gabatar da sabon shirinta na dabaru wanda ke da nufin sake nazarin tsarin kasar game da nahiyar Afirka.
Wallafawa ranar:
Italiya a wannan kokari na fatan ganin ta cimma daya daga cikin abubuwan da gwamnatin Giorgia Meloni ta sa gaba, wanda ya kamata ya mayar da ita a matsayin babban jigon kungiyar G7 da za ta shugabanta a watan Yuni mai zuwa.
Italiya na fafutukar ganin ta kafa kanta a matsayin mai iko a tekun Bahar Rum, musamman dangane da bakin haure.
Daya daga cikin makasudin sabon shirin na gwamnati shi ne magance tushen tattalin arzikin da ke haifar da kwararar bakin haure daga Afirka zuwa Turai, tare da yawan bakin haure a Italiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu