Isa ga babban shafi

Mutane dubu 15 sun mutu a birni guda na Sudan sakamakon kashe-kashen kabilanc-Rahoto

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce tsakanin mutane dubu 10 zuwa dubu 15 ne aka kashe a wani birni guda da ke yammacin yankin Darfur na Sudan a shekarar da ta gabata sakamakon rikicin kabilanci tsakanin dakarun kai daukin gaggawa na RSF kungiyar ‘yan tsagera na kabilun yankin. 

Dimbim 'yan gudun hijira ne suka tsallaka zuwa Chadi daga yankin Darfur na Sudan.
Dimbim 'yan gudun hijira ne suka tsallaka zuwa Chadi daga yankin Darfur na Sudan. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Rahoton da aika aike wa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ce da taimakon majiyoyi masu tattara bayanan sirri ne aka samu alkalumman wadanda suka mutu a birnin El Geneina.

Alkaluman wadanda aka kashe ya yi hannun riga da wanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayar, wanda ke nuni da cewa mutane dubu 12 ne suka mutu a fadin kasar Sudan. 

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane dubu 500 ne suka tsallaka Sudan zuwa gabashin kasar Chadi mai nisan kilomita da dama daga kudancin Amdjarass  don neman mafaka daga kashe-kashen da ake yi a yankunansu.

Wata kungiya mai tattara bayanai a kan yake-yake ta ce a tsakanin watan Afrilu da Yunin shekarar da ta gabata, birnin El Geneina ya fuskanci matsanancin rikici, tana mai zargin rundunar RSF da abokanta da kisan ‘yan kabilar Masalit a hare-haren da ka iya zama laifukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.