Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta sake murkushe yunkurin kifar da gwamnatin Traore karo na 4

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta sanar da murkushe wani yunkuri na wargaza tsaro da zaman lafiyar kasar bayan kawar da barazanar wata manakisa da aka shirya don kifar da gwamnatin Kyaftin Ibrahim Traore.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore kenan. © AFP
Talla

Kakakin gwamnatin Sojin ta Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, ya bayyana cewa tuni aka kame mutanen da ke da hannu a yunkurin ranar Alhamis, wadanda yanzu haka ke amsa tambayoyi masu alaka da cin amanar kasa.

A cewar kakakin gwamnatin tun a ranar 14 ga watan Janairun nan ne aka yi yunkurin wanda ya kunshi wasu tsaffin sojoji da kuma wadanda ke bakin aiki sai wasu kungiyoyin farar hula dama daidaikun fararen hular wadanda suka hada baki don wargaza tsaron kasar.

Sanarwar da gwamnatin Sojin ta Burkina Faso ta fitar ta ce ta datse duk wata hanyar shigar kudi ga kungiyoyin fararen hular da ke da hannu a wannan yunkuri, kazalika ta kame tarin fararen hular da ke hannu duk da cewa bata fadi cikakken alkaluman mutanen da kamen ya rutsa da su ba.

Kakakin gwamntin ta Burkina Faso ya ce sashen leken asiri da na fikira na ci gaba da sanya idanu tare da laluben duk wadanda ke da mummunan shir ikan gwamnatin Sojin kasar.

Wannan dai shi ne yunkurin juyin mulki na 4 ga gwamnatin Sojin ta Burkina Faso karkashin jagorancin Ibrahim Traore wanda ya kwaci mulki a watan Satumban 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.